Idon Kukai Karatu Zaku Samu Daukaka A Duniya: Wahida Isma'il

Wahida Bilyaminu Isma'il

Wahida Bilyamin Ismail Matashiyar lauya wacce ta ce tana gama makarantar sakandare ta sami gurbin karatu a jami’ar Bayero University Kano domin karanta aikin lauya. Inda mu a lokacin mu samun shiga jami’a bai da wahala idon dai har kaci jarabawar WAEC da JAMB.

Wahida ta ce fannin da ta so ta karanta kenan, kuma ta samu tunda abinda ranta ke so kenan ba tare da ta fuskanci wata matsala ba, illa dai a wancan lokaci suna shiga makaranta da safe wajen karfe takwas da jajircewa da mai da hankali ta kammala karatun ta cikin nasara.

Ku Duba Wannan Ma Rashin Biyan Bashi Ga Mai Karamar Sana'a Babbar Illa Ce - Maryam Mu’azu

Wahida ta kara da cewa tana kammala karatun jami’ar, ta samu aikin gwamnati, kuma ba ta sami wata matsala da abokan aiki maza ba illa dai yar matsala da ta fuskanta a farkon fara aikin ta shine da yake su lauyoyin gwamnati ne kafin ta saba da kotun ya dauke ta lokaci kadan.

A karshe ta ce babu abinda ya kai kammala karatun boko akan lokaci dadi, ba ayi wasa ba, ta kara da cewa, "Idan kukai karatu zaku samu dukkanin wata daukaka ta duniya, za’a dinga sha’awar ka gami da alfari da kai a cikin al’umma."

Your browser doesn’t support HTML5

Idon Kukai Karatu Zaku Samu Dukkanin Wata Daukaka Ta duniya: Wahida Bilyaminu Isma'il