Idan Aka Ba Matasanmu Dama Zasu Nuna Hazaka Da Basirar Su: Oga Kumbo

Ghali Abdullah, Gali DZ

"Kishin zuwa wasu jihohin dake makwabtaka da mu domin samun masu daukar video ko hoto mai kyau ya sa na dukufa aikin daukar hotuna da video mussamam ma ga mawaka masu tasowa"

Ghali Abdullah, wanda aka fi sani da Gali DZ, ko Oga Kumbo, ne ya bayyanawa wakiliyar DandalinVOA, ya ce a yanzu haka ya dukufa harkokin daukar hotunan bidiyo, da sauransu a yunkurinsa na samawa matasa ayyukan yi

Matashin ya bayyana cewa ya shiga harkar camera da editin ne bayan da ya lura cewar mafi akasari idan ana neman hoto, ko video, mai kyau har sai an tafi wata jiha kafin a samu biyan bukata wanda matasa da ke karkararmu da cike da dinbin hazaka da basira wanda da zarar an basu dama zasu fito da iyawarsu.

Ghali Dz, ya ce akalla ba’a kasara ba yana da matasa guda bakwai da ke aiki a karkashinsa banda wasu guda goma sha biyar da yake baiwa aiki a yau da kullum.

Kumbo DZ, ya kara da cewa burinsa na dogaro da kai a harkar Kannywood da fagen mawaka yana so ya samar da wata dama da a cikin garin Kanon Nijeriya, za’a bigi kirji a ce akwai kamfani da zai bada hoto mai kyau da inganci.

Your browser doesn’t support HTML5

Idan Aka Ba Matasanmu Dama Zasu Nuna Hazaka Da Basirar Su: Oga Kumbo