Ibrahim Abdullahi Wada: Tsarin Daukar Aiki A Najeriya bana Zamani Bane

Ibrahim Abdullahi Wada

Tsarin daukar ma'aikata a kasar Najeriya al'amari ne wanda yake da daure kai, domin a wasu lokutan mutane su kanyi masa kirari da "wa-kasani wa-yasanka".

Babu shakka idan muka duba yadda kasar Najeriya ke daukar ma'aikata zamu iya yarda da wannan fadi na jama'ar kasar, ba don komai ba, saboda yadda ake turereniya tun daga lokacin sayar da form, har izuwa sanda za'ayi jarrabawar karshe. Amma kuma abin mamaki sai kaga wanda bai sha wata wahala daga cikin wadannan jerin wahalhalunba, yasamu aikin, musamman idan yana da wani dan'uwa babban ma'aikaci a kasar.

Tabbas tsarin daukar ma'aikata a Najeriya yasha bamban da yanayin tsarin daukar ma'aikata a kowacce kasa da 'yan kasar suka samu wayewa ta zamani, musamman idan mukayi duba da abin kunyar da ya faru a 'yan kwanakin da suka gabata alokacin jarrabawar daukan ma'aikatan shige da fice na kasar, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wanda daga karshe har gwamnati ta yanke wani hukunci na soke wannan jarrabawa. Bayan haka kuma gwamnatin tace ta baiwa duk wanda yasamu rauni tikitin zama ma'aikaci ba tare da wata jarrabawaba, wanda hakan yajawo yan kasar suke ta kace-nace akan al'amarin.

A ganina babu wani abu da gwamnatin kasar zatayi da yawuce soke wannan jarrabawa domin canja wani sabon tsari da ya dace, sai dai kuma maganar bada tikitin samun aikin da gwamnatin ta bayar. Shin gwamnatin tanada tabbacin ingancin majiyyatan wadanda tabawa tikitin? Amsar itace Ah ah! Domin wannan aikin aikine dake bukatar tantancewa mai yawa. Idan kuwa hakane tayaya za'ayi wannan hukunci?

Kasar Najeriya kasace mai yawan jama'a wanda hakanne makasudin kawo wannan cinkoso da ya jawo mutuwa da jikkatar wasu manema aiki, amma kuma yawan jama'ar kasar ba zai taba zama uzuri ba idan mukayi duba sauran kasashen duniya wadanda suka fi kasar Najeriyar yawa wadanda basu taba samun wani abu makamancin hakan ba.

Ina ganin idan gwamnatin kasar zata bi tsare-tsaren da zan rubuta akasa za'a samu saukin faruwar abubuwa makamantan haka.

YIN ZIYARAR AIKI DON GANO TSARE-TSARE NA WAYEWA:
Kamata yayi gwamnatocinmu su ringa fita ziyarar aiki kasashen da suka cigaba don ganin yadda suke gudanar da aiyyukansu cikin tsari ba tareda hayaniya ba.

SAMARDA KAYAN AIKI NA ZAMANI:
Yakamata gwamnati ta samar da kayayyakin aiki na zamani don gudanar da dukkan ayyukanta cikin sauki komai yawansa batare da ansamu matsala ba, domin kuwa a kasashen da sukaci gaba ba'ayin irin wannan cinkoso sakamakon sun wadatu da kayayyakin aiki na zamani, zakayi jarrabawar batareda samun matsala ba.

TABBATAR DA INGANCIN SHUWAGABANNIN MA'AIKATU KAFIN ABASU AIKI:
Yakamata idan gwamnati zata bada mukamai kamar mukamin minista, ko wani shugaban wata ma'aikata kamar shugabancin ma'aikatar shige-da fice, gwamanati ta tabbatar da ingancin wannan shugaba kafin ta bashi aiki batare da tasaka siyasa, bambancin addini ko bangaranci aciki ba.

WANZAR DA CIKAKKEN TSARO:
A duk lokacinda za'a gudanar da abu irin wannan yakamata a samarwa da gurin da za'a gudanar da wannan abu cikakken tsaro da sanyawa duk wanda ya halacci wannan guri, kwanciyar hankali don kaucewa samarda faduwar gaba da guje-guje tsakanin mahalatta taron.

---------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------

Sakonni da Masu Amfani da Shafi Suka Aiko

Muryar Amurka da Shafukan yanar Gizo masu dauke da bayanai, na iya barin masu anfani da kafar su rubuta ra’ayoyinsu su saka abubuwan da suka rubuta su yi sharhi, su aika da sakonni da hotuna da zane-zane da saka labarai da ma ire-irensu a matsayin bayanai da masu amfani suka aiko. To sai dai ka amince cewa duk abun da ka rubuta zai bi namu hanyar sadarwa ko wasu da muke muamala da su, su yi a madadinmu da yanar gizo. Ka amince cewa Muryar Amurka da kafar Sadarwa ta Yanar Gizo kafofi ne na anfanin jama’a ba hanyoyin sadarwar mallakar wasu ba ne.

Kana iya aiko da bayanai kamar wato abubuwan da ka rubuta wa Murya Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo wadanda mallakarka ne, wato kai ne ka rubuta, ko kuma kana da izinin marubucin ka yadasu ta yanar gizo. Ba zaka karya dokar da ta hana satar abun da wani ya rubuta ba ko ka hana wani hakkin gudunmawarsa game da rubutun wanda ya hada da ikon mallaka kamar sunan da wani ya yi rajista dashi domin aikin ko tambari da yake anfani da shi. Haka ma ba zaka saci asirin sana’arsa ba ko na kansa ko na talla. Ka yarda kuma ka tabbatar kai ne kake da iko da kuma izinin yin anfani ko yada ayyukan kuma ka baiwa Muryar Amurka izinin yada abun da ka rubuta.

Ka adana duk wata shaidar mallaka da kake da ita bisa ga duk ayyukan daka sa a Muryar Amurka da kafar Sadarwar Yanar Gizo. Amma domin ka baiwa Muryar Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo, to ka baiwa VOA ikon mallaka ita kadai na har abada ba tare da biyan wani haraji ba. Kuma zata yi anfani da shi duk fadin duniya, ta iya kofa, ko ta baiwa wani ko ta yi masa ‘yar kwaskwarima a yi anfani da shi a bainar jama’a da yin anfani da shi ta wasu hanyoyi daban daban.