Janar Babangida, wanda ya zanta da manema labarai albarkacin cikarsa shekaru 75 yau Laraba, yace “A shekarar 1999, munyi kokarin mayar da Majalisu su zama na wucin gadi, domin rage yawan kudaden da ake kashewa akansu.”
Kalaman tsohon shugaban dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar Wakilan Najeriya ta dauki zafi akan batun aringizon kasafin kudi. Daya daga cikin ‘yan Majalisar daga jihar Neja, Bala Faruk Bidda, ya tabbatar da cewa akwai tabargazar kudaden a Majalisar, ya kuma ce akwai shaida da take nuna barnar kudin da akayi.
Yan Najeriya dai na jiran ganin an dauki mataki akan lamarin Majalisar, kamar yadda Alhaji Lawali Shukura ke kira ga mahukunta na bangaren Shari’a da su tsaya su yi aikinsu tsakani da Allah, domin taimakawa gwamnati wajen farfado da halin da kasa ke ciki.
Saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.
Your browser doesn’t support HTML5