Ibada Ko Nishadi, Samari Da 'Yan Mata Wajan Sallar Tahajjud

A yau dandalinVOA ya waiwayi dabi’ar nan da samari da ‘yan mata ke yi a lokacin da ake gabatar da sallar tahajjud , Mal Abdullahi ya ce wannan dabi’a ce da aka dade ana yi, dan haka lokaci ne da samari da ‘yan mata ke mayar da hankali wajan zance ko free call a maimakon yin ibada da kara kusanci ga ubanji.

Ita kuwa Zainab cewa ta yi wannan rashin tarbiya ne kuma laifin iyaye mata ne na rashin cusa wa ‘ya’yansu muhimmancin ibada mussaman ma a loakcin ramadana.

Shima Abdallah, cewa yayi rashin samun walwala da wasu ‘yan mata ke da shi a gidajensu ke sa da zarar sun sami fita sai su raja’a cikin dabi’un da basu dace ba.

Akan batun ne har ila yau muka sami zantawa da Mal Muktar Umar Sharadda, Limamin masallacin juma’a na rijiyar zaki – ya ce wannan yana daga cikin rudi na shaidan, domin ya hana mutum samun rahamar Allah, sannan ya ja hankalin musulmi da su sani cewar ramadana daya ne a shekara sannan dan Adam bashi da tabbacin cewar zai kai wani ramadana.

Daga karshe ya bayyana cewar watan Ramadana wata ne na neman rahamar ubangiji da gabatar da wasu bukatu na dan adam, dan haka ya ja hankalin iyaye da matasa su ji tsoron Allah, su kauce ma aikata abubuwa marasa kyau.

Your browser doesn’t support HTML5

Ibada Ko Nishadi, Samari Da 'Yan Mata Wajan Sallar Tahajjud