ZABEN 2015: Hukuncin Saye da Sayar da Katin Zabe

Na'urar Karanta PVC.

Shin wane hukunci gwamnatin Najeriya ta dauka game da masu saye da sayar da katin zaben 'yan kasa na din-din-din? Wakilin Muryar Amurka ya hada mana wannan rahoto game da wannan batu

Hukumar zabe dai bata fadi hukuncin da za a yiwa wanda aka kama yana sayar da katin ba in ka dauke cewa da suke sayar da katin mummunar matsalar rashin sanin ‘yanci ne ga masu sayarwa. Shima shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega cewa yayi aikin baban giwa ne ko da mutum ya sayi katin zaben wani domin na’ura ba zata yarda da yin zaben da katin wani ba.

Ya kara fadawa wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya cewa sai dai in wanda ya sayar din za a dauko ya dangwalawa wanda ake so. Inji Jega ya fada yana ‘yar dariya. Wani mai sharhin al’amuran yau da kullum Dakta Sadik Abubakar Gombe kuma sakataren Jam’iyyar SDP, ya nuna cewa kila ana yin haka ne don cutar da al’umma ya yi kira ga jama’a da su yi zabe na gari.

Shima Solomon Dalong cewa yayi bait aba ganin sayar da ‘yanci mai araha kamar wannan ban a saida katin zabe. Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin siyasa Ahmad Gulak kuwa, karyata cewa yayi wai ‘yan PDP ne ke saye. Yace APC su suka kirkiro sharrin hakan. Sannan yace har ma ‘yan APC din sun sayo na’urar da zata iya hana na’urar zaben yin aikinta idan suka ga wajen da ake zaben ba a zabarsu.

Shi kuwa Kakakin hukumar zaben Najeriya Nick Dazang yace, laifi ne sayarwa da sayen katin zabe, kuma tuntuni yana cikin dokokin zaben kasar. Yace akwai cin tarar naira dubu 500 ko daurin shekaru 2 a gidan yari ko kuma duk hukuncin guda biyu a lokaci guda ga mai saye ko sayarwa. In dai ba a manta ba bincike ya nuna mafi yawanci ‘yan Najeriy a na rayuwa ne a kasa da dalar Amurka 1 a rana.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2015: Hukuncin Saye da Sayar da Katin Zabe-2'30"