Kundin tsarin kare hakkin marubuta na kasa, ya tanadar da hukunci mai tsanani ga duk wanda ya karya dokar tsarin.
Dr. Usman Shu’aibu Zunnuraini, na jami’ar Bayaro da ke Kano, yayi Karin haske dangane da irin hukuncin da aka tanada ga masu karya dokokin satar fasaha na rubutun kirkira, yace akwai hukumar da hakkinta ne ta dinga duba irin wadannan masu sace sace kuma idan aka samu mutun da wannan dabi’ar to za’a kwace duk abun da ya sata kuma za’a hukuntar da shi dai dai da abun da ya aikatar don akwai hukunci a matakai daban daban.
Zakuma a iya sama mutun tara mai yawa don hukuntashi akan abu da ya aiwatar, baya ga haka mutun na iya zuwa gidan kaso a sanadiyyar wannan aiki na satar basira.
Kuma mutane su sani idan har mutun ya wallafa kasidarshi to yakamata ya garzaya wajen sama mata kariya na satar basira wanda wannan hukumara ta Copy Right a turance, ko gidan da ke buga kasidu don su bashi lambar da ake badawa na mallaka, ta haka idan wani ya satar maka rubutu to kana da damar kaishi gaban kuliya.
A karshe yayi kira ga marubuta da suyi kokarin bin duk hanyoyi da suka kamata wajen kare aikinsu da zarar sun kamala rubutunsu don gujema bata gari masu satar rubutu.