Hukuncin Daurin Shekaru Biyar Na Jiran Masu Satar Jarabawar WAEC

  • Ibrahim Garba

Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta tanaji daurin shekaru biyar ko tarar N200,000 ga duk wanda ya saba ma dokar WAEC
Ministar Ilimin Nijeriya, Furfesa Rukayya Rufa’I, ta bayyana cewa Gwamnatin Taryyar Nijeriya ta yanke shawarar cewa daga yanzu duk wanda ya keta dokar jarabawar WAEC zai shafe shekaru biyar a gidan yari ko kuma zabin biyan tarar Naira N200,000 ko kuma duka biyu.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukunci Mai Tsanani Na Jiran Masu Satar Jarabawar WAEC



Wakilinmu a Abuja, Umar Faruk Musa y ace Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yanke wannan shawarar ce a zaman Majalisar Zartaswa na baya-bayan nan.

Minista Rukayya ta ce hukuncin zai biyo bayan duk wani nau’in karya dokar yin wannan jarabawar, kama daga dalibin da ya saci jarabawa zuwa jami’in da ya taimaka aka sace jarabawa a kilas dinsa zuwa wanda ya rubuwa ma wani jarabawa zuwa kuma wanda ya fitar da tambayoyin jarabawar tun kafin lokacin da dai sauransu.