Hukuncin Da Kotun Koli Ta Yanke Kan Zaben Osun Ya Kada Mu – PDP

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta ce ta kadu matuka da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke kan wanda ya lashe zaben jihar Osun.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, jam’iyyar ta PDP ta ce “rarrabuwar kawunan da aka samu a tsakanin alkalan kotun kolin, alama ce da ke nuna cewa da walakin goro a miya.”

A jiya Juma’a kotun kolin ta yanke hukunci kan takaddamar da ake yi kan zaben na gwamnan jihar ta Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, wanda aka yi a 2018.

Hukumar zaben jihar ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Gboyega Oyetola a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Amma a watan Maris, kotun sauraren korafe-korafen zabe ta ayyana Sanata Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP a matsayin asalin wanda ya lashe zaben.

Sai kuma ga shi kotun koli ta mayarwa da Oyetola da nasararsa a jiya Juma’a.

Amma biyu daga cikin alkalan kotun kolin bakwai sun nuna ba su gamsu da hukuncin kotun ba.

“Rarrabuwar kawunan da aka samu tsakanin alkalan ya nuna akwai walakin goro a miya kan wannan batu.” Inji sanarwar ta PDP.

“Abin farin cikinmu a nan shi ne, ba wai kotun kolin ta kore batun da muka yi ba ne da wanda miliyoyin ‘yan Najeriya suka yi cewa, dan takararmu Sanata Ademola Adeleke ne ya lashe zaben, ta yanke hukuncin ne bisa wasu matsaloli da aka fuskanta a kotun korafe-korafen zaben.”

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar ta PDP, Atiku Abubakar, wanda shi ma yake kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammad Buhari ya samu a zaben watan Fabrairu, ya nuna takaicinsa kan hukuncin kotun kolin.

“Ina mai nuna cikakken goyon baya ga masu yi wa Najeriya fatan alheri tare da fadawa Sanata Ademola Adeleke da al’umar jihar Osun cewa, muna tare da su a duk irin halin da suke ciki.”