Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, musamman malamai da ‘yan gwagwarmayar ‘yancin mata da kananan yara na cikin wadanda ke ci gaba da mayar da martani game da matakin kotun wadda ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani dattijo dan shekaru 70 bayan samun sa da laifin yin fyade ga wata yarinya ‘yar shekara 12 .
Hukuncin na zuwa ne kwana biyu bayan wata kotun shari’ar Musuluncin ta yanke makamancin wannan hukunci ga wani matashi dan shekara 22 bisa laifin batanci ga manzon Rahama, Annabi Muhammad S.A.W.
Baya ga irin ce-ce ku-cen da ake ta yi kan shafukan sada zumunta ga masu mabambantan ra'ayoyi, kungiyoyi da cibiyoyi su ma sun tofa albarkacin bakinsu.
A cewar kungiyoyin masu fafutukar 'yancin mata da kananan yara sun dade suna fafutukar ganin an fara daukar tsauraran matakai ga masu aikata laifukan fyade.
Hajiya Hauwa Elyakub, daraktar gidauniyar Elman Nafi’an mai tallafawa ilimin kananan yara a nan Kano ta sheda wa Muryar Amurka farin cikinta game da lamarin yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi wa wata karamar yarınya fyade.
"Mun dade muna so a aiwatar da irin hukunce-hukuncen saboda irin abubuwan mutanen nan suke aikatawa, dole a zartar da hukuncin."
Sai dai a daya bangaren Malam Musatafa Dandume, wani malamin addinin Islama ya ce zartar da hukunci irin wannan na nuna koma baya a tsakanin Musulmi.
"Duk da cewa wannan hukuncin ya yi dai-dai karkashin adinin Islama, amma fa ya kamata mu gane cewa shi fa Musulunci so yake a hana barna ba wai a kashe mutane ba, mafita shi ne mu dawo baya mu gyara kanmu da tarbiyarmu," a cewar Mustafa.
An saba yanke hukunce-hukunce ga mutane a Najeriya amma maganar ta shashance bayan kwana biyu, lamarin da ya sa mutane ke ta jiran su ga ko za a aiwatar da hukunce-hukuncen a karshe.
Saurari rahoton a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5