Hukumomin Uganda sun cafke manyan jami'an jaridar Red Pepper

Yadda mahukuntan Uganda ke kama wadanda kasar ta zarga da cin amananta

Manyan 'yan jaridar Red Pepper dake Uganda su takwas sun shiga hannun hukumomin kasar ranar Talata bisa zargin cin amanar kasar

Hukumomin kasar Uganda, sun cafke manyan jami’an gidan jaridar Red Pepper su takwas inda ake tuhumarsu da laifin cin amanar kasa.

‘Yan sanda ne suka far ma ofishin gidan jaridar mai zaman kansa wacce ake wallafa ta da harshen ingilishi a daren ranar Talata, suka kama ‘yan jaridar, wadanda aka zarge su da rubuta wani labarin kanzon-kurege a ranar Litinin.

Labarin wanda ya ruwaito wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba, ya nuna cewa shugaba Uganda Yoweri Museveni na shirin ya kifar da gwamnatin Rwanda da Paul Kagame ke jagoranta.

Baya ga tuhumar ta cin amanar kasa, ana kuma tuhumar ‘yan jaridan da laifin wallafa “labari mai tunzurarwa wanda ka iya yin barazana ga tsaron kasa,” a cewar mai magana da yawun ‘yan sanda Emilian Kayima a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sai dai hukumomin na Uganda ba su fadi takamaimai ranar da za a gurfanar da ‘yan jaridan a gaban kotu ba.