Hukumomin Turkiya Sun Cafke Wanda Ya Kai Hari Ranar Karshen Shekara A Istanbul

Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan

Rahotanni daga kafofin yada labarai a Turkiyya sun ce an kama wani da ake zargi shine ya kai hari akan wani klub ya kashe mutane 39 ranar 31 ga watan Disambar bara.

Jaridar da ake kira Hurriet Daily News tace hukumomi sun tsare wani mai suna Abdulkadir Masharipov jiya Litinin a gundumar Esnyurt. Dansa mai shekaru hudu yana nan lokacinda aka kama shi.

Wata tashar talabijin a kasar da wasu kafofin yada labarai sun ce an kama mutumin ne yayinda aka kai samame a wani gida inda yake zaune da abokinsa daga Kyrgyzstan. Haka nan an tsare wasu biyar dake gidan, cikinsu har da mata uku, an mika yaron ga hukumomi masu kula da yara.

Rahotannin suka ce 'Yansanda sun gane inda wanda ake zargin yake tun a makon jiya, amma suka jinkirta daukar mataki domin su kiwaci zirga zirgarsa da kuma wadanda yake mu'amala dasu.

Ana sa ran 'Yansanda zasu bada karin bayani a safiyar yau a taron d a zasu yi da manema labarai.

Jaridar Hurriet, ta ambaci wata majiyar 'Yansanda a makon jiya tana cewa Masharipov ya iso Istanbul ranar 15 ga watan Disambar bara daga lardin Konya domin ya shirya kai harin.