A wani rahoto mai shafi 409 da kungiyar ta fitar na shekarar 2016 tace azabtarwa da jami'an tsaro keyi kan kaiga mutuwar wadanda ake tuhuma.
Shugaban kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Afirka ta Yamma Awal Musa Rafsanjani shi ya jagoranci gabatar da rahoton.
Inji Rafsanjani rahoton ya nuna cewa har yanzu akwai wasu dokoki da yakamata Najeriya ta sa hannu domin ta kyautata hakkin bil Adama da walwalar jama'a. Wadannan dokoki har yanzu Najeriya bata rabtaba masu hannu ba.
Rafsanjani ya cigaba da cewa har yanzu jami'an tsaron Najeriya basu daina take hakkin bil Adama ba a kasar. Haka kuma, inji Rafsanjani mummunar akidar nan ta kisan gilla tana nan daram dam.
Har wa yau kungiyar ta zargi 'yansandan dake bin sawun 'yan fashi da makami da ake kira SAS da sabawa 'yancin jama'a ta hanyar kama mutane barkatai.
Jami'in hulda da manema labarai na kungiyar ta Amnesty International reshen Najeriya Isa Sanusi yayi tsokaci. Yace abun da suke cewa shi ne idan an tura sojoji suna anfani da karfin da ya wuce kima. Yace kamar rikicin Boko Haram sun ga duka bangarorin biyu suna taka hakkin bil Adama. Sannan kuma mutane miliyan biyu rikicin ya rabasu da muhallansu. Ban da haka wadanda suke sansanonin 'yan gudun hijira suna rayuwa ne a cikin hali na galabaita.
Isa Sanusi ya cigaba da cewa kwanakin baya wata kungiya tayi bincike ta gano ana cin zarafin mata da suke zaune a sansanonin.Sau tari kuma aka samu rahotanin dake cewa yunwa tana kashe yara kanana.
Ya kira a tashi tsaye domin akwai matsala ta yunwa da matsanancin hali na rayuwa. Ta fannin kiwon lafiya ma da ilimi an samu matsala. Yakamata a ga cewa an dawo da mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa matsugunansu a garuruwansu.
Amma ga jakadan kasar Faransa a Najeriya wanda aka bada rahoton a idanunsa yana cewa yaji wani gwamna ya fada cewa sama da shekaru talatin ke nan ana kashe mutane amma ba'a taba kama kowa ba. Yace wannan na nuni da cewa akwai abun da ba'a yi daidai. Shawararsa ita ce a fito a yi tsayin daka wajen tabbatar da doka da oda domin a kare hakkokin mutane
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5