Wata yarinyar da ta ki tayar da bama-baman da ‘yan Boko Haram su ka turata ta tayar, mai suna Zahra’u, ta ce uwayenta ne su ka kai ta daji wurin ‘yan Boko Haram sai ‘yan Boko Haram su ka kira ta da wasu ‘yan mata biyu gefe guda, su ka tambayi kowacce ko za ta yi “Istishadiyya?” Sai ita Zahra’un ta tambaye su ko mene ne “Istishadiyya” sai su ka ce ma ta kunar bakin wake. Su ka ce to za ta yi? Sai ta ce a’a.
Wakilnmu a Kano da ya aiko da wannan rahoton, Mahmud Ibrahim Kwari, ya ruwaitota ta na cewa sun ce ma ta idan fa ta aikata kunar bakin waken to labudda za ta shiga Aljannah, kamar yadda za ta shiga Aljannah muddun ta iya suratul Qaaf, ko kuma ta na idar da Sallah cikin lokaci da karatun Alkur’ani da Salatul Khauf. Su ka ce amma idan ta ki to za su harbe ta ko kuma su sa ta a rami su hallakata kamar yadda su ke ma masu laifi.
Zahra, ta ce dajin na zagaye ne da ‘yan Boko Haram din kuma duk macen da ta yi yinkurin gudu za su harbe ta. Sai su ka ce za su harbe ta muddun ta ki yadda ta yi Istishadiyyar, sai ta ce to. Da aka tambaye ta yadda aka yi ta je dajin, sai ta ce mahaifinta ne ya kaita da ita da mahaifiyarta.
Da aka tambaye ta abin da ya faru bayan da ita da sauran ‘yan kunar bakin wake biyun su ka iso Kantin Kwari, sai ta ce da su ka iso Kano sai aka sa su cikin Keke NAPEP (Nafe) aka kai su kasuwar Kantin Kwari. Sai dayarsa ta ce rarrabuwa za su yi. Kuma dayar ce za ta fara shiga ta tayar. Idan ta tayar sai kuma ita da Zahra’u su shiga su tayar da nasu bama-baman. Sai dayar ta shiga, sai mai maganar ta ce ita ma da Zahra’un su shiga; sai su ka shiga. Sai ta ce da ita da Zahra’u su tayar da na su bama-baman, sai Zahra’u ta canza ra’ayi ta ki, ta ce ma ta ba za ta tayar ba. Sai ta tayar da na ta, “har ya same ni na ji ciwo.
Sai na bar wajen na je bakin kwalta na sanar da Nafe (Keke NAPEP)” Sai ta ce ya kai ta Dawanau saboda ta san Dawanau din sun taba zama wurin (duk dayake ita yar asalin Damaturu ce). Ta ce da aka kai ta Dawanau, sai matan makotan gidan da su ka taba zama din su ka fito, sai y ace to ya na neman wani wakili don akaita asibiti. Ya gaya ma su abin da ya faru. Sai su k ace mazansu bas a nan kuma ba kowa. Anan nan sai ga wani dattijo can zai wuce, sai wata yarinya ta ce aiko ga wani kaza can (ta fadi sunansa), sai aka ce ta kira shi, sai ta kira shi, ya zo aka kai Zahra’u asibiti. An fara mata aiki har an dinke ma ta ciwo kenan, sai mai Nafe (Keke NAPEP) din ya zo ya ce ya ga wani abu a Nafe din shi, kuma na ta ne. Sai su ka yi wa sojoji waya. Sojoji su ka zo su ka dauke ta cikin mota su ka tafi da ita. Da aka tambaye ta ko mene ne ta bari cikin keke nafe din sai ta ce bama-bamai ne.
Your browser doesn’t support HTML5