Hukumar lafiya ta duniya da ake kira WHO ta fadi cewa kasar Tanzania ta kasa maida martani akan bukatar bayannan wasu mutane da ake kyautata zaton su na dauke da cutar Ebola.
A wata sanarwa, hukumar ta fadi cewa ta sami rahotanni amma ba a hukumance ba akan yiwuwar mutane da yawa sun kamu da cutar Ebola a wurare daban-daban a kasar dake gabashin nahiyar Afrika.
Sanarwar ta kuma ce wasu mutane da aka gano sun yi mu’amulla da wani da ake kyautata zaton ya kamu da cutar a birnin Der es Salaam, an sami labarin cewa an killacesu a wurare daban daban a kasar.
Hukumar ta ce dan bayanin da aka samu a hukumance daga hukumomin Tanzania ya zama da kalubale wajen nazarin hadarin dake tattare da yanayin cutar.
Jami’ai a kasashen gabashi da tsakiyar Afrika na zama cikin shirin ko ta kwana akan cutar ta Ebola. Su na kokari su ga sun dakile bazuwar cutar da aka sami barkewarta a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo har mutane sama da 2000 suka mutu tun daga watan Agusta.