Malaman addinin Islama a Najeriya sun ce matakin da kasar Saudiyya ta dauka na tantance Hadisan Manzon Allah (SAW) zai taimaka matuka wajen shawo kan matasan musulmai dake hankoron shiga kungiyoyin ta’addanci.
Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar IZALA a Najeriya, ya ce baicin shawo kan masu tunanen shiga ta’addanci, matakin zai taimakawa dalibai masu neman ilmi da zasu karu da wasu hanyoyi da dama. Ya bayyana cewa tantance Hadisan ba wai za’a canza wani abu ba ko a kawo sassauci kuma ba domin Amurka za’a ba. Ya ce sai an samu malamai na kirki da zasu ba da fatawa da zai taimakawa mutane.
Shi ma jigon darikar Tijjaniya a jihar Neja, Imam Shehu Rimaye, bayan ya nuna gamsuwa da matakin na Saudiyya, ya ce babu wani hadishin da ya amince da a je a yi aikin ta’addanci ko kuma ya koyas da ta’addanci. Ya ce akwai bukatar gyara na gaske.
Mustapha Nasiru Batsari na da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5