Yayin da aka samu bullar kwayar cutar coronavirus a wasu kasashen Afrika a makon jiya hukumomi a jamhuriyar Nijer na ci gaba da karfafa matakan zuba ido a fiyalen jiragen sama da kuma kan iyakokin kasar domin riga kafin wannan annoba da ke ci gaba da hallaka mutane a sassan duniya.
Kawo yanzu, babu wanda aka gano dauke da cutar coronavirus a jamhuriyar Nijer amma duk da haka hukumomin kiwon lafiya na ci gaba da zuba ido akan muhimman wuraren kai da kawon matafiya da nufin dakile dukkan wata barazana kamar yadda ministan kiwon lafiyar Nijer Dr. Iliassou Idi Mainasara ya bayyana wa manema labarai a yau litinin.
Haka kuma hukumomi na gargadin jama’a akan kada su guji abokan huldarsu ba tare da samun wata kwakwarar hujja daga wajen likitoci ba.
Bayanan da ake yadawa yanzu haka a kafafen sada zumunta na bayyana cewa an gano magungunan dake warkar da cutar coronavirus, abinda Dr. Baruani Ngoy Bienvenu na reshen hukumar lafiya ta duniya a Nijer yace maganar banza ce.
Likitan ya ce a kimiyance ba su da masaniya idan an samu irin wadannan magungunan.
Haka kuma wasu na cewa kwayar cutar coronavirus ba ta iya jurewa yanayin zafi, wannan maganganu ne marasa tushe, domin kwayar cutar virus abu ne da ke rayuwa a cikin wata halitta ta daban.
A saurari cikakken rahoto a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5