Masana kiwon lafiya a kasar sun ce cikin yara hamsin za'a samu talatin da cutar cizon sauro ta kamasu.
Sabili da haka ne a wannan shekarar gwamnati ta dauko manyan matakai na shawo kan lamarin. Misali, za'a yi kemfen na bada maganin rgakafin ciwon kafin yaro ya kamu da ita. Yara daga masu wata ukku zuwa shera daya ne zasu fara cin gajiyar maganin.
Wadanda suke tsakanin shekara daya zuwa biyar su akwai irin maganin da za'a basu na kwana ukku jere da zai karesu na wata guda ciwon bai kamashi ba. Bayan wata guda za'a koma a sake raba irin maganin kyauta har tsawon watanni hudu.
Gwamnati ta gano cewa cikin wata hudu na damina ne yara ke kamuwa da cutar.Wato za'a cigaba da bada maganin daga wannan watan na Agusta har zuwa watan Nuwamba ko fiye ma.
Baicin kashe yara da yawa cutar cizon sauro na sa mata bari da kuma kawo karancin jini ga mace mai haihuwa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5