Cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren dindindin na ma’aikatar cikin gida, Dokta Oluwatoyin Akinlade, ya bayar a madadin, ministan harkokin cikin gida, Hon Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya daukacin al’umar Musulmi murnar zagayowar wannan rana.
Ya kuma yi kira gare su, da su kasance masu nuna hakuri da juriya wadanda suna daga cikin dabi’un Manzon Allah S.A.W.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ministan na taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da na kasashen waje murnar riskar bikin na bana.
Eid-ul-Maulud biki ne da Musulmi ke yi a duk shekara don nuna murna ga zagoyar wannan rana.
Bikin na Maulidi na dauke da tarukan wa’azi, da addu’o’in yabon Manzon Allah S.A.W., karatun al-Qur'ani da kuma yin sadaka.