Hukumomin Mulkin Sojan Nijar Sun Kuduri Aniyar Sake Rubuta Tarihin Kasar

Janar Abdourahmane Tiani, tare da wadansu jami'an sojojin Nijar

Tsama tsakanin kasar Faransa da Jamhuriyar na kara zafafa, yayinda sojojin da ke mulki a kasar suka kuduri aniyar sake wallafa tarihin kasar.

Bayanai na nuni da cewa, hukumomin suna neman sake wallafa tarihin kasar ne sabili da wanda a ke amfani da shi a halin yanzu a makarantun boko na kasar bai da cikakken bayanin tarihin kasar da zai amfani masu tasowa.

Masana tarihi da kuma masu kula da lamura sun bayyana goyon bayana wannan matsayin.

A hirar shi da Muryar Amurka, Lawali Mahamand Salisu na a jami'ar Tahoua ya yaba wannan kudurin da ya ce zai zama da amfani a makarantu. Malam Lawali ya bayyana cewa, "Idan ka yi la'akari da abin da ake koyawa a makarantu, abin kunya ne. Duk an san tarihin Shugabannin kasashen yammacin duniya, amma ban da na Sarakunan gargajiya na kasarmu".

A nashi bayanin, Nuradine, malamin tarihi mai karantarwa a wata tsangaya a cikin garin Tahoua, yace mafi yawancin tarihin da ake koyawa daliban kasar na karkata ne ga abubuwan da suka wakana shekaru aru - aru a yammacin duniya, maimakon maida hankali kan gwarzayen kasar da suka yi fafutukar ganin kasar ta girku shekaru da yawa da suka shude.

Mani Bassiru, shugaban kungiyar malaman koyarwa ta USES Nijer kuwa yana ganin wannan mataki da hukumomin mulkin sojan kasarsuka dauka zai sa yaran kasar su san tarihin kasarsu.

"Lallai wannan wani mataki ne da muka yi na'am da shi, idan yaran mu suka san tarihin kasarsu da abubuwan da suka faru a kasar.

Malam Nouridine ya ce sanin tarihin kasarka na da muhimmanci sosai, saboda zai sa mutum ya rike kan shi da daraja, ya san yadda rayuwar gabata ta kasance.

Tuni dai, hukumomin mulkin sojan kasar suka kafa kwamitin da zai share fage don rubuta tarihin kasar, bisa la'akari da al'adu addinai, zamantakewa da fafutukar da gwarzayen kasar suka yi a baya.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Mulkin Sojan Nijar Sun Kuduri Aniyar Sake Rubuta Tarihin Kasar