Hukumomin Mali Na Bin Diddigin Harin Da Aka Kaiwa Sojan Faransa

Hukumomin kasar ta Mali na can suna bin diddigin harin da aka kai jiya Lahadi a kan wata tawagar sojan Faransa masu sinitiri a kasar ta Mali, inda har mutane hudu suka rasa rayukkansu.

Hukumomin kasar ta Mali na can suna bin diddigin harin da aka kai jiya Lahadi a kan wata tawagar sojan Faransa masu sinitiri a kasar ta Mali, inda har mutane hudu suka rasa rayukkansu.

Ma’aikatar tsaro ta Mali ta tabattarda cewa ko bayan wadanda aka kashen, har ila yau an raunata wasu kamar 20, ciki harda sojojin Faransa guda takwas. Rundunar sojan Faransa ta tabattarda cewa ba’a kashe mata soja ko daya ba lokacinda aka tada bam daga cikin wata mota a garin Gao.

Har zuwa yanzu dai ba wata kungiyar da ta dauki alhakin kai farmakin wanda ya faru kwannaki kalilan bayanda wasu ‘yan jihadin Islama suka abkawa helkwatar sojan tarbacce na kasashen Afrika dake Bamako, inda nan ma mutane shidda suka rasa rayukkansu.