A jihar lamarin bangar siyasa sai kara ta'azzara ya keyi, sabili da haka ne dan majalisar dattawan Najeriya Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya shirya wani taron bita a Kontagora, akan mahimmancin sanin al'adun jama'a da kuma dorewar zaman lafiya.
Alhaji Abdullahi Ara, shi ya wakilci Sanatan a wurin taron bitar, ya ce lokaci yayi da matasan ya kamata su yiwa kansu karatun ta natsu. Injishi matasa su ne inji motar siyasa, saboda haka dole ne su falka daga barci su san abun da ya dace, da kuma yakamata su yi. Ya gargade su kada su bari a yi anfani dasu su ci mutunci wani ko su shiga kone kone.
Alhaji Tanko Baba Ahmed, mai baiwa gwamnan jihar shawara akan harkokin addinai, ya gabatar da jawabi inda ya ce taron ya zo daidai lokacin da matasa basu da aikin yi sai fitina ga kuma zabuka sun kusa. Injishi sau tari ana anfani da matasa wajen aiwatar da barna da tashin hankali.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana jin dadinsu. Wani ya ce kowannen su an bashi Nera dubu hamsin wanda zasu iya bude wata sana'a da ita maimakon neman tashin hankali.
A saurari karin bayani a rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Your browser doesn’t support HTML5