Hukumomin Jihar Adamawa Sun Shirya Taron Bita kan Yaki da Cutar Zazzabin Cizon Sauro

Taro kan zazzabin cizon sauro da yankunan da Boko Haram ta mamaye

Hukumomin kiwon lafiya a jihar Adamawa sun kaddamar da taron bita na fadakar da mutane yadda zasu yaki cutar zazzabin cizon sauro musamman a yankunan da suka taba zama karkashin mamayar 'yan Boko Haram

Zazzabin cizon sauro wato malaria na cikin manyan cutututtukan dake addabar jama’a musamman mata da kananan yara a Najeriya, kuma kamar yadda alkalumman hukumomin kiwon lafiya ke nunawa, kusan kashi 97 cikin dari na mata masu juna biyu da kuma kananan yara a kasar na dauke ko kuma sun kamu da cutar, kuma lamarin yafi kamari a yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa.

Duk shekara, biliyoyin Naira ne ake kashewa da zimmar yakar cutar kuma kawo yanzu da alamun da sauran rina a kaba.

To sai dai don samun nasarar yaki da cutar ta hanyar anfani da gidan sauro ne ma yasa hukumomin kiwon lafiya a jihar Adamawa tare da tallafin wasu kungiyoyi masu zaman kansu shirya taron bita ga ‘yan jarida inda aka tabo rawar da ya kamata yan jarida zasu taka don yaki da cutar cizon sauron.

Baya ga matsalar rashin tsaftar muhalli, yanzu haka rikicin Boko Haram ya maida hannun agogo baya a yaki da cutar, musamman ganin cewa tun shekarar 2010 ba’a samu damar raba gidan sauro ba a yankunan da ake fama da rikicin na Boko Haram.

Dr Bwalki Dilli dake zama Daraktan kiwon lafiya a matakin farko na Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta jihar Adamawa ya bayyana matakin da suka dauka ayanzu a jihar inda yace zasu raba gidajen sauro kyauta kuma za’a bi gida-gida don kwalliya ta biya kudin sabulu.

Shi ko tun farko da yake jawabin maraba, Mr Issac M.Kadala dake zama jami’in kula da shirin yaki da cutar Malaria a jihar Adamawa, yace dole a hada hannu wajen yaki da cutar.

Hukumar kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dai na cewa babu hanya mafi sauki wajen yaki da cutar maleriyan kamar ta amfani da gidan sauro, musamman a yankunan karkara da nan talakawa yan “rabbana ka wadata mu” ke rayuwa!

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Jihar Adamawa Sun Shirya Taron Bita kan Yaki da Cutar Zazzabin Cizon Sauro - 3' 38"