Hukumomin Ilmi a Nijar Sun Bukaci Majalisar Dokokin Kasar Ta Kare ‘Yan Mata

Firayim Ministan Nijar

Rashin hukumta masu lalata da ‘yan mata dake karatu ya sa hukumomin ilimi a Jamhuriyar Nijar shigar da bukatar kafa dokoki na musamman da zasu hukumta irin masu bata ‘yan matan makarantu

Lura da wasu miyagun dabi’un dake faruwa da wasu ‘yan mata dalibai ba tare da hukumta masu aika aikar ba, ya sa hukumomin ilmi shigar da bukata a gaban Majalisar Dokokin Jumhuriyar Nijar domin nazarin batun da zummar samar da kariya ga ‘yan mata domin su samu karatu mai dorewa.

Ministan ilmi a matakin firamare, Dauda Muhammad Marde, yace idan yarinya ta shiga makaranta a barta ita ma ta zama mutum. Ya nuna jin takaicin ganin cewa a kasar akwai wasu jihohi dake aurar da ‘ya’yansu da zaran sun kai shekaru 13 da haihuwa.

Kungiyoyin ci gaban ilmi na cikin wadanda suka gabatarwa Majalisa bayanai domin fadakar dasu akan bukata da kuma dalilan da ilmin mata ke tabarbarewa a Nijar.

Audu Mamman Lokoko, shugaban wata kungiyar jama’a, ya ce sau tari ‘yan matan da ya kamata a ce suna makaranta su ne suke talla ana yi masu fyade. Wasu ma da ya kamata su kula dasu su ne suke yi masu ciki. Sai dai abun takaici wanda ya yiwa yarinya ciki ba’a damu dashi ba sai yarinyar da ta dauki cikin. Irin wannan lamarin ne ya kamata Majalisa ta duba, inji Lokoko.

A saurari karin bayani daga rahoton Souley Barma

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Ilmi a Nijar Sun Bukaci Majalisar Dokokin Kasar Ta Kare ‘Yan Mata -2' 48"