Hukumar tsaron kasar Ghana tana daukan matakan yin zabe cikin kwanciyar hankali.
Ma'aikatar 'yansandan Ghana ta fito da tsare-tsare na hadin gwiwa da jama'ar kasar ganin yadda ake anfani da matasa wurin tada tarzoma lokacin zabe. Ma'aikatar ta zauna da shugabannin matasa na jam'iyyun siyasar kasar cikin wannan makon inda ta bayyana masu matakan zaman lafiya da take dauka a zabe mai zuwa.
Yayinda yake jawabi a wurin taron da matasa babban sifeto na 'yansandan John Kudalo ya gargadi matasan yana cewa su tabbatar da 'yan jam'iyyunsu sun gujewa sabawa doka. Yace ba zasu yadda da duk wani nauyi na 'yan tsaro kamar yadda jam'iyyun siyasa suka saba yi ba a lokacin zabe. Yace zasu fito da kashedi da kuma lokacin da wani rukunnin tsaro na 'yan siyasa bai kamata ya yi aiki ba.
Samuel Auku shugaban matasan babbar jam'iyyar hamayya ta NPP ya kalubali wasu kalamun babban sifeton 'yansandan. Yace idan 'yansanda na son matasa su tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana su ma 'yansandan su bayyana irin rawar da zasu taka kuma su ba kowa damar shiga koina a cikin kasar. Kada su hana wani shiga wani bangare na kasar.
Shi ma Duvani Nkurma na jam'iyyar hamayya na PPP ya bayyana matakan da jam'iyyarsa ke dauka. Yace sun riga sun gargadi mambobinsu cewa idan wani ya yi abun da bai dace ba zasu mikashi ga mahukunta su hukumtashi.
Sidi Abubakar Musa na jam'iyyar NDC mai mulki ya maida hankali kan zaben. Yace babu wata jam'iyya da zata lashe zaben saboda tana da goyon bayan hukumar zabe. Duk wanda yake son lashe zabe sai ya je kasa cikin jama'a. Yace koda shugaban 'yan hamayya yake shugabancin hukumar zabe sai sun lashe zaben.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5