Cafke mutanen ya biyo bayan wani samame ne da jami'an tsaro suka kai cikin garin Agadez da kewayensa a wani matakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsanaki a jihar ta Agadez.
Mutanen da aka cafke ana zarginsu ne da safaran miyagun kwayoyi da suka hada da koken da tamol da dai sauransu. Wasu kuma cikinsu ana zarginsu da mallakar miyagun makamai da suke anfani dasu wajen yin fashi a hanyoyi da afkawa jama'a tare da kwace dukiyoyinsu
Abis Idrisa Muhammad mataimakin mai shigar da kara a jihar Agadez yace mutane ne da sun yi Allah wadai da dokokin kasa suna aikin asha. Yace suna sayar da kwayoyi. Suna sayarda bindigogi kana su amshewa mutane kayansu. Suna kwacewa mutane motoci
Kwayar wiwi da suke sayarwa daga kasashen dake makwaftaka da Nijar suke samota.
Sama da bindigogi goma ne aka kama a samamen.
Wakilin gwamnan jihar Agadez Sadu Saloke ya kira al'umma da su bada hadin kai wa jami'an tsaro domin cimma nasarar ayyukansu. Ya kira mutane su dinga bada labari idan sun ga mutane suna shigowa.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5