NIGER, NIGERIA - Rahotanni sun nuna yadda a yanzu haka mazauna garin na Lokoja ke zaune cikin wani yanayi na zullumi saboda yadda wadannan matasa da akasarinsu ‘yan shekaru 15 zuwa 17 ke ci gaba da aukawa jama’a da muggan makamai tare da kisan mutane da satar dukiyar jama’a da kuma kona gidaje.
Wasu mazauna garin na Lokoja sun ce daga safiyar Litanin din nan zuwa ranar Talata wadannan matasa sun kashe mutane hudu tare da kona gidajen jama’a a unguwar Kabawa dake birnin Lokoja.
Mai baiwa gwamnan jihar Kogin shawara akan harkokin tsaro kwamanda Duro Jerry Omodara ya shaidawa manema labarai cewa gwamnati ba za ta zura idanu tana gani wadannan matasa suna tada hankalin jama'a ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogin tace ta cafke mutane 17 da ake zargin suna da hannu a wannan aika-aika inji kakakin ‘yan sandan Mr. Wilans Aya.
A yanzu dai rahotanni sun tabbatar da cewa mazauna unguwar Kabawar a birnin Lokoja na ci gaba da barin gidajensu domin tsira daga wadannan matasa masu muggan makamai.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5