Babban kotun kasar Rasha ta tabbatar da dakatar da shugaban ‘Yan adawa Alexi Navalny daga shiga takarar shugaban kasa.
Zaben dai za ayi shine a cikin watan maris mai zuwa.
Babban kotun ta amince da bukatar hukumar zaben kasar wato Central Election Commission na shawarar data yanke cewa ta dakatar da Navalny sabo zargin sa da akeyi da aikata ayyukan assha.
Sai dai Navalny shi da magoya bayan sa sunce wannan dakatarwan ba kome bane illa tsagwaron siyasa.
Akan haka ne Navalny ya kira ‘yan kasar da su fito domin gudanar da zanga-zanga a ranar 28 ga wannan watan kafin lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa.
Bayanai na cewa ga bisa dukkan alamu shugaba maici Vladimir Puttin ne zai iya sake lashe zaben domin wani waadin shekaru 6.
Navalny yace Putin wanda ya kwashe shekaru 17 kan karagar mulki a matsayin shugaban kasa da Prime Minista ya kamata ace ya sauka yaba wasu wuri.
Yace alhali ma farin jinin Putin ya dogara ne ga yawan farfagandar kafar yada labarai na gwamnati da kuma hukumar zaben kasar data hana wasu ‘ya kasa da suka cancanta tsayawa takara.
Puttin wanda tsohon dan hukumar KGB ne, zai tsaya takara ne a matsayin dan takarar je kai da halin ka.
Abinda masu kula da harkokin siyasa ke cewa zai kara masa tagomashi sabanin dan takarar jamiyya na jeka nayi ka.