Hukumar Zaben INEC Ta Ce Ta Yi Tanadi Domin Nakasassu

Hukumar zaben INEC  ta Najeriya ta gana da shugabannin hadakar kungiyoyin nakasassu, a wani yunkuri na ganin an fadakar  da nakasassun sabbin matakan da aka tanadar musu a babban zabe da ke tafe a Najeriya.

An kwashe shekara da shekaru hadakar kungiyoyin guragu, da makafi, da kutare da kurame da kuma bebaye ke kokawa kan yadda ake maida su saniyar ware a wasu harkokin cigaban kasa, ciki harda batun zabe.

A wajen wani taron tuntuba da nakasassun suka shirya, hukumar zaben INEC tace an tanadi hanyoyin da suma zasu sami damar kada kuri'arsu kamar sauran jama'a a wannan karon. Barr. Kassim Gana Gaidam, kwamishinan hukumar INEC a jihar Adamawa ya tabbatar da hakan.

Kamar sauran nakasassu, ita ma Godiya Simon tace a da, har sun fidda tsammanin za a dama da su.

"Tabbas taro ya kayatar, ganin yadda hukumar zaben ta tuna da mu da wannan sabon tsarin. Gaskiya mun yi farin ciki sosai. Ai kaji abin da suka ce na tanadin da aka yiwa masu larura, muna fatan wannan zai tabbata,” a cewar Godiya.

Ba a kammala taron ba sai da masu fama da larurar suka yaba da sabuwar dokar da ta basu dama kamar kowa a Najeriya, sun kuma koka akan yadda wasu ke nuna masu wariya ko kyama ta hanyar kiransu da sunan nakasassu, batun da jami'in yadda labaran hadakar kungiyoyin masu bukata ta musamman Alhassan Ibrahim yace daga yanzu ba zasu lamunce ba.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zaben INEC Tace Tayi Tanadi Domin Nakasassu - 3'37"