Hukumar Zabe Tana Ragistan Mutane Domin Bada Katin Zabe Na Dindindin

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.

Hukumar Zabe ko INEC a takaice ta soma ragistan mutane domin bada katin zabe na dindindin kafin zaben shekarar 2015.
Hukumar zabe ko INEC a takaice ta kasa jihohin kasar ta Najeriya zuwa rukuni uku domin samun yin aikin ragistan mutane cikin natsuwa da inganci tare da gujewa irin matsalolin da hukumar ta fuskanta can baya.

Jihar Taraba na cikin jihohin da hukumar ta fara aiwatar da ragistan mutane. Kwamishanan zaben jihar Mr.Othniel Oje shi ya jagoranci aikin ragistan na wannan shekara. Yace zasu fara ragistan ne da 'yan Najeriya da shekarun haihuwarsu suka kai goma sha takwas bayan zaben 2011.

Amma wasu manazarta kamar irin su Muhammed Ismail tuni suka soma harsashen cewa wasu matsaloli kamar harkar rashin tsaro da rashin hanyoyin kaiwa ga kauyukan dake cikin tsaunuka da duwatsu ka iya kawo cikas. Mutane da yawa ba za'a iya kai garesu ba balantana a yi masu ragista. Lamarin zai fi tsamari a jihohin dake cikin dokar ta baci. Yace babu yadda za'a gama aikin cikin kwana hudu domin wasu kauyuka dake kan iyaka a Borno ,Gombe da Adamawa ba za'a kai garesu ba cikin kwanakin da aka ce za'a yi aikin. Akwai wurare da dama inda jama'a suna cikin tashin hankali.

Jiha kamar Adamawa jiha ce dake da dimbin duwatsu.Akwai garuruwa da dama da a kan kwashe kwanaki uku ko hudu kafin a kai garesu ko da ma basa cikin dokar ta baci balantana ga dokar ta baci. Da wuya cikin 'yan kwanakin da INEC ta bayar a ce an kaiga wadannan kauyukan har a yiwa mutane ragista, ke nan mutane da yawa a jihohin dake cikin dokar ta baci ba zasu samu su yi ragista ba ko yin zabe.

A can baya irin wannan aikin ya fuskanci matslolin da suka shafi naurori da rashin gudanar da aiki yadda ya kamata. Amma a wannan karon INEC tace ta dauki matakan kaucewa matsalolin.

Kwamishanan zaben jihar Adamawa yace da yaddar Allah matsalolin ba zasu kai na baya ba. Yace kullum suna karuwa da ilimi. A cikin sabon shirin INEC zata raba katin zabe mai kama da katin fitar da kudi daga banki wanda a ke kira ATM. Wannan katin shi ne na dindindin wanda zai dade ya kai shekara goma.

Bayan an raba katin za'a yi ragistan wadanda da can basu yi ba da kuma wadanda suka samu matsaloli.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zabe Tana Ragistan Mutane Domin Bada Katin Zabe Na Dindindin - 3' 09"