A wata sanarwa da hukumar ta bayar a rubuce tace daga daya ga wannan watan har zuwa hudu ga watan ta hana hawan babur kowane iri ne a garin Gombe.
Sanarwar ta samu sa hannun kakakin hukumar wato DSP Kwaja Attajiri inda yace yin hakan ya biyo bayan tashin bama bamai a wurare biyu da suka hallaka 'yan kunar bakin waken dake dauke dasu.Kakakin yayi karin bayani da shirin da su keyi na tarbar manyan baki biyu a garin.
Lamarin ya faru ne daidai da lokacin da ake cewa shugaban kasa zai isa garin. Kakakin 'yansandan yace shirin zuwan shugaban kasan yana nan ba'a dageshi ba. Shugaban kasa mai ci yanzu zai ziyarci garin yau kana tsohon shugaba wato Buhari shi ma ya isa garin jibi.
Ya kira jama'a kada su yadda wasu su batasu domin mutanen jihar Gombe mutane ne masu son zaman lumana.
Dangane da tashin bama baman Attajiri yace an fara bincike kuma zasu shaidawa jama'a abun da bincikensu ya gano
Wani ganao yace akalla mutane uku ne suka mutu tare da wani mai sayar da rake.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5