A cikin wata wasika mai shafi hudu dauke da sa hannun babban sufeton ‘yan sandan Ghana (IGP), Dokta George Akuffo Dampare, hukumar ta nuna cewa rubutun da jakadar ta yi a kafar sada zumunta bai dace ba kuma ya nemi ya bata darajar hukumar ‘yan sandan Ghana.
Hukumar ‘yan sandan Ghana ta bukaci jakadiyar Birtaniya a Ghana, Harriet Thompson, da kada ta shiga harkokin da bai shafe ta ba.
Hakan ya biyo bayan Rubutun da jakadar ta yi akan shafinta na kafar sada zumunta ta twita dake cewa, “an sake kama Oliver Barker-Vormawor, mai fafutukar #FixTheCountry, na fahimci cewa (an kama shi ne) domin karya dokar hanya, a hanyarsa ta zuwa kotu. Zan yi sha'awar ganin inda wannan zai kai ”.
Wasikar ta jaddada cewa alakarsu da mai fafutukar ta dace da manyan dokokin kasar, domin haka maganar da jakadiyar ta yi, “ba shakka an yi ta ne daga wani matsayi na son rai ko kuma rashin fahimta.”
Jakadiya Hariet Thompson ta fito a gidan telebijin na GHone dake Accra inda ta ta yi karin bayani cewa hukumar bata fahimce ta ba. “Ya tabbata daga abinda ya faru ba a fahimci abinda ake nufi ba, kuma ba lallai bane sai na mayar da martani ga IGP ba”. A cewarta, ba ta wa wani mugun nufi a sakon da ta isar.
Masana da manazarta sun saba a kan ko matakin da sufeto janar din ‘yan sanda ya dauka na bayyana korafinsa ya dace.
Shugaban tsangayar ilimi a kwalejin dakarun Ghana, Dakta Vladmir Antwi Danso, da sanannen dan jarida Kwesi Pratt, duk sun goyi bayan matakin da hukumar ta dauka.
Malami a jami’ar koyan aikin jarida dake accra, Zakariya Tanko Musa, a nasa bangaren ya shawarci hukumar ‘yan sanda da ta mika korafinta ta hanyar ma’aikatar harkokin kashashen waje, amma ba ta wasika da za ta bayyana ga sauran jama’ar gari ba.
Masani kan tsaro da dangatakar kasa da kasa, Irbad Ibrahim ya yi kira ne da a yi taka tsan-tsan wajen tunkarar lamarin.
Shi dai Oliver Barker-Vormowor, hukuma na tuhumarsa da yin barazana ga tsaron kasa, wanda a sanandiyar haka aka kama shi a farkon shekarar nan kuma a ka ba da belinsa a watan Afrilu.
Rahoto na nuni da cewa ma’aikatar harkokin kasashen waje ta shiga cikin lamarin.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullahi Bako cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5