Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko M-D-D tace ta soma rarraba kayan masrufin ceton rayukkan mutane sama da 6,000 da ke cikin mawuyacin hali a jihar Tekun Yei ta kasar Sudan ta Kudu.
WASHINGTON DC —
Sai dai kuma wadanda ake son rabawa kayan agajin sunce yayinda suke godiya da marhabin da taimakon, sun fi son a taimaka a maida su kauyukkansu don su koma su girbe kayan anfanin dake cikin gonnakinsu.
Hukumar ta ‘Yan-Gudun Hijiran tace mutane fiyeda 10,000 ne suka rasa gidajensu a sanadin tashin hankalin da ya barke tsakanin sojan gwamnati da magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar, Reik Machar.
Halin da irin wadanan ‘yan gudun hijiran ke ciki ya kara tsananta ne saboda an hana wa kungiyoyi da ma’aikatan bada agaji iya kutsawa zuwa cikin yankunan da ake rikici a cikinsu.