Magunguna da dama suna kan gwaji a fuska ta uku kana muna sa ran za a samu magunguna masu inganci da zasu taimaka wurin kare mutane daga kamuwa da cutar. Koda yake har i yau ba a samu mafita ba kuma tana yiwuwa ba za a samu ba, inji babban darektan WHO Dr. Tedros Adhanom, yana fada a wani taron manema labarai a jiya Litinin.
Adhanom ya yi kira ga kasashe da daidaikun mutane kowa ya bada taimakon da zai iya wurin gwaji da bibiyar masu cutar da nesanta da juna da kuma saka abin rufe baki da hanci, da ma wasu abubuwa masu muhimmanci da zasu taimaka wurin dakile cutar.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da kamuwa da cutar da mace mace daga COVID-19 ke kara yawa a fadin duniya. Ya zuwa jiya Litinin, an tabbatar da mutum miliyan 18 da dubu dari biyu ne suka kamu da cutar, a cewar cibiyar nazarin coronavirus ta jami’ar John Hopkins, lamarin da ya kai wadanda suka mutu da cutar zuwa dubu 691 da dari uku.