An dauki tsawon lokaci a Jamhuriyar Nijar wajen kulawa da kuma bada magani kyauta ga mata masu juna biyu, musamman a lokacin haihuwarsu, don rage mace-macen da hakan ke haddasawa.
To kwatsam sai ga labarin soke wannan tallafi da suke samu daga wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya. Mutanen Jamhuriyar ta Nijar sun bayyana tashin hankalinsu matuka game da janye wannan tallafi da ya dau tsawon shekaru ana yi.
Wasu mazauna kasar sun yi kira ga gwamantinsu da ta yi duk mai yiwuwa wajen nemo wani sabon tallafin daga ko ma ina za a iya samunsa a duniya domin ci gaba da wannan aikin ceton rayukan masu dauke da juna biyu.
Wakilinmu a Nijar Haruna Mamman Bako ne ya aiko mana da wannan rahoton da yake manne a makalar kasa.
Your browser doesn’t support HTML5