Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta kasashen Turai UEFA,
ta ce ta amince zata fara amfani da fasahar nan ta mataimakin
alkalin wasa na bidiyo, wato (VAR) a gasar zakarun turai ta kakar shekara ta 2019/20, haka kuma a gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai da za'a
yi a shekarar 2020.
Hukumar ta UEFA ta ce a kakar wasa ta 2020, da kuma 2021, za a soma amfani da wannan fasahar mai taimakawa alkalin wasa a gasar Europa, da
kuma na cin kofin UEFA, wato Super Cup, wanda take shiryawa.
Matakin da UEFA ta dauka na yin amfani da fasahar maimaicin bidiyo a wasannin da take shiryawa, ya biyo bayan nasarar da aka samu ta amfani da
fasahar a yayin gasar cin kofin duniya na bana da aka gudanar a Rasha 2018, yadda ya taimakawa alkalan wasa wajan gano wasu abububuwan da suka shige masu duhu a lokutan da ake wasa.
Your browser doesn’t support HTML5