Hukumar UEFA Ta Kirkiri Sabuwar Gasar Zakaru Ta UEL2

Hukumar kula da shirya gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai (UEFA) ta tabbatar da cewar an kirkiro sabuwar gasa ta uku, wadda zata baiwa wasu kungiyoyi kwallon kafa damar buga babbar gasa a matakin nahiyar, domin su samu damar nuna kansu a duniya.

Kwamitin zartarwar hukumar ta UEFA ce ta sanar da wannan matakin da ta dauka bayan wani taron da tayi a Dublin, babban birnin Jamhuriyar Ireland inda aka cimma matsaya kan sabon kudirin ta.

Sabon sauyin shi ne, daga kakar wasa ta 2021 zuwa 2022 da za’a soma sabuwar gasar da aka mata lakabi (UEL2), wato UEFA Europa League 2, hukumar za ta rage yawan kungiyoyin dake buga tsohuwar gasar Europa League daga kungiyoyi 48 zuwa 32.

Wannan sabon shirin zai baiwa manyan gasannin Turai da suka hada da na Zakarun Turai Uefa Champions League, Europa League, da kuma sabuwar gasar ta UEL2, damar tsara fafatawa tsakanin kungiyoyi 32 ko wane bangare.

Bisa tsarin Uefa na sabuwar gasar ta UEFA daga shekarar 2021 kungiyoyin kwallon kafa da suka kare a matsayi na 7, daga manyan gasannin kasashen Turai, sune zasu samu damar shiga gasar da za’a gauraya su da wasu kungiyoyin da za su fito daga kananan gasannin na nahiyar Turai.

Za'a buga gasar ta UEFA Europa League 2, kamar yadda ake Europa a ranakun Alhamis.