Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Nahiyar Turai UEFA, ta yanke hukunci akan kasar Serbia na buga wasu wasaninta ba tare da 'yan kallo ba (closed doors) ciki harda wanda za tayi da Luxembourg.
UEFA tace hukuncin ya biyo bayan samun magoya bayan Serbia ne da nuna wariyar launin fata, a wasan da su kayi da Portugal na neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar kasashen Turai na shekarar 2020, inda aka doke ta da ci 4-2 ranar 7 ga watan Satumbar bana a Belgrade.
A ranar 14 ga watan Nowamba 2019, Serbia zata karbi bakoncin kasar Luxembourg, cikin gasar neman gurbin shiga wasannin Nahiyar kasashen Turai na 2020.
Haka zalika an ci tarar hukumar kula da wasan kwallon kafa na kasar Serbia, kudi har fam dubu £23,550 a sakamakon sakaci da su kayi a wasan Serbia da Portugal, inda magoya baya suka shiga cikin filin wasa da kuma jefa wasu abubuwan, da kunna wuta a filin yayin wasan wanda haka ya saba wa dokokin wasanni.
Serbia dai tana matsayi na uku ne a rukunin B, da maki goma cikin wasanni shida da ta buga.