Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kashe Fina-Finan Hausa - Mubarak Abba

Mubarak Abba

Mubarak Abba ya ce hukumar tace-fina-finai ta jihar kano ta kashe fina-finan Hausa inda dole ta sa masu shirya manyan fina-finai suka koma shirya fina-finai domin gidan talabijin da silma.

Ya ce tun bayan ziyartar Dandalinvoa da yayi a baya gwamnati ta yi yunkurin tsaftace masana’antar sai dai a cewarsa akwai ‘yar takura sakamakon ka’idojin da hukumar tace fina-finai ta sanya.

A yanzu dai sai dai masu harkar fim suyi sam barka domin an shawo kan yan downloading ta hanyar daina sakin fim, domin kuwa duk abinda ya shafi dan fim ya shafi dan downloading.

Ku Duba Wannan Ma Shin Akwai Yiwuwar Hollywood Zasu Gayyaci Shah Rukh Khan Kuwa?

Ya ce babu wani abin mamaki na samun canji da aka yi a yanzu, don haka dole ne masana’antar Kannywood ta sauya salon tallata hajarta, misali na sanya fim a silma a yanzu ya zama wajibi su samo wasu hanyoyin da zasu baiwa al’ummarsu damar kallon fina-finan su sabanin sauyin zamani da aka samu na sanya fina-finai a silma.

Ya ce a yanzu duk dan fim din da ya kashe fiye da kudi Naira Miliyan biyar lallai zai tafka asara muddin mai shirya fim bai kai fim din gidan silma ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kashe Fina-Finan Hausa - Mubarak Abba