Hukumar Tace Fina-Finai Ta Dauki Matakan Dakile Satar Fasaha - Iyantama

Hamisu Lamido Iyantama

Na koma masana’antar Kannywood kasancewar kasuwar ta gyaru da kuma irin matakan da hukumar tace fina-finani da kannywood suka dauka domin lalubo hanyar da za’a dakile tare da magance matsalolin masu satar fasaha inji Jarumi mai shirya fina-finai Hamisu Lamido Iyantama.

Iyantama, ya ce harkar fim kamar wata babbar masana’anta ce da ke da fanoni da dadama, kuma ta kasance an zabe shi a matsayin shugaban kwamitin da aka kafa don dakile satar fasaha.

Jarumin ya bayyana cewa ya kafa wani kwamiti da zai tsara yarda kasuwar ‘yan downloading zata wakana tare da shigo da su masana’antar domin kowa ya karu.

Ya kara da cewa tuni suka zauna da ‘yan downloading kuma sun amince da wannan sabon kudiri, a cewarsa wannan ita ce hanya daya da za’a dakile satar fasaha, domin masu fim su samu riba sabanin yadda abin yake a da.

Iyantama ya ce, da farko yakan fito a matsayin jarumi ko furodusa sai ya canza sheka inda ya koma fanin jarida ya ke kuma tallata hajjar fina-finan kannywood, inda ya ce satar fasaha ce ta kore shi daga masana’antar a wancan lokaci.

Daga karshe Iyantama ya baiyana cewa a wancan lokaci maimakon su samu riba sai dai su fadi wanda hakan ne yasa ya hakura a wannan lokaci.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Tace Fina-Finai Ta Dauki Matakan Dakile Satar Fasaha - Iyantama