Baya ga tabbatar da cewa, kayayyakin masana’antun Najeriya na gogayya dana kasashen duniya, sabon shirin auna kayayyakin yayi dai-dai da daftarin yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen Afrika mai tanadin cewa, lallai sai kayayyakin da ingancin su suka cimma mizanin da ake bukata ne za’a fitar dasu domin sayarwa.
Yayin kaddamar da wannan shiri a Kano, Darakta Janar na hukumar tabbatar da Ingancin kayayyaki ta Najeriya SON Alhaji Faruk Salim yace sun sawo sababbin na’urori akan daruruwan miliyoyin naira, domin ganin cewa, burin hukumar na karfafawa masana’antun Najeriya gwiwa su rinka samar da kayayyaki da kasuwar duniya zata shi ya samu nasara.
Yace da-ma tun a baya sun yiwa kamfanonin alkawarin samar da injina na zamani da za’a rinka auna aikace-aikacen su da kayayyakin da suke karba daga ‘yan kasuwa da kuma wadanda suke sarrafawa, gabanin fitar dasu kasuwanni, domin a tabbatar da cewa, an samu yanayi na ba cuta kuma babu cutarwa tsakanin masu saye da masu sayarwa.
Kamfanoni 8 ne hukumar ta SON ta zaba wajen kaddamar da wannan sabon tsarin awo, kuma Dr Ibrahim Muhammad Gerawa dake zaman manajan Darakta rukunin kamfanonin Gerawa, gudan cikin wadanda aka zaba, yace ba karamin tasiri wannan sabon tsari zai yi ba ga aikace-aikacen su.
Yace duk da cewa, suna da sikelin da suke amfani dashi wajen awon kayayyakin su, tsarin da hukumar S.O.N ta zo dashi zai kara kare muradun su da na abokan huldar su.
Wani babban al’amari dake damun ‘yan Najeriya shine yawaitar kayayyakin jabu a cikin Najeriya da akan shigo dasu daga ketare, amma babban daraktan hukumar SON yace suna hada gwiwa da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki domin dakile wannan matsala.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5