Jami’an sufuri a birnin London sunce ba zasu sabunta lasisin kamfanin tasi na Uber a birni ba, sabili da matsalar tabbacin kare lafiyar fasinja.
Cibiyar kula da harkokin sufuri ta birnin London-TFL ta fada a wata sanarwa yau jumma’a cewa, Kamfanin Uber a London bai cancanta ya gudanar da harkoki a birnin ba.
Cibiyar tace take-taken kamfanin Uber da kuma yadda yake gudanar da ayyukansa yana da rauni a fannoni da dama dake da barazana ga lafiyar fasinja da kuma harkokin tsaro.
Daga cikin batutuwa da cibiyar TFL ta ambata akwai batun aikata miyagun laifuka da kuma amfani da fasahar zamani wajen hana hukumomi sa ido a manhajar.
Kamfanin Uber yace shawarar da birnin London ya yanke na hana amfani da manhajar manuniya ce cewa birnin baya sha’awar hulda da kamfanoni dake amfani da fasahar zamani.
Kamfanin ya kuma ce zai kalu balanci wannan hukumcin.