Babban kontirolan hukumar shiga da fice na kasa Alhaji Abdullahi Dikko Inde ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishin hukumar dake Kano. Wakilin Muryar Amurka ya tambayi shugaban shin ko ina jami’an su suke har wadannan kaya suka shigo ta iyakar kasa zuwa cikin gari sannan aka kama su?
Inda shugaban ya amsa da cewa, “ai abinda Hausawa sukace mai son abinka yafi ka dubara, kuma kamar yadda kuka sanine shi wannan fasa kwauri duk duniya babu inda aka kawar da shi” shugaban dai ya cigaba da bayanin cewa suna yin aikin su dai dai gwargwado.
A bayanin shugaban ya nuna cewa wannan wata hikima ce ta ma’aikatan Kwastan, domin a kwai dokar da ta tanada cewa zasu iya zuwa shiga kowanne guri idan har suna zargin an keta doka ba tare da takardar waren ba, dalilin daya sa kenan suka bari aka tara kayan dayawa kafin su kama kenan.