Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa reshen jihar Filato, ta horas da matasa kan illolin da suke tattare da shaye shayen miyagun kwayoyi domin yadda zasu amfani kansu da al’ummar su.
Taron bitar da aka yiwa shugabannin matasa daga unguwanni daban daban na jihar Filato, ya jaddada muhimmancin amfani da karfi da basirar da matasan keda ita wajan inganta rayuwarsu da kuma al’ummar su domin ci gaban kasa.
Jami’in hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Filato Mr Bello Mumuni, ya ce matsalar shaye shaye ta yi Kamari a tsakanin matasa, lamarin da ke haddasa husuma da kashe kashe da barnata dukiyoyi.
Ganin yadda shirye shiyen zaben kananan hukumomi ya kankama a jihar Filata wakiliyar sashe Hausa na Muryar Amurka, Zainab Babaji ta sami zantawa da matasa da dama akan yadda zasu kaucewa yaudarar ‘yan siyasa duba da yadda suke amfani da su wajan tada hankulan al’umma domin biyan cimma manufar su ta siyasa.
Shugaban hukumar wayar da kan jama’a ta kasa reshen jihar Filato, Mr Bulus Dabit, ya ce sun horas da matasanne domin su koma gida su horas da sauran matasan da ke yankunan su.
Your browser doesn’t support HTML5