Hukumar dake kula da kwallon kafa ta tarayyar Najeriya NFF, ta bukaci tawagar 'yan wasan Najeriya Golden Eaglets, ta doke takwararta kasar Ghana a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika ta CAF U17 2018 wadda akeyi a Jamhuriyar Nijar inda tayi alkawarin karin kudi ga 'yan wasan in har sun dauko kofin.
Kwamishinan fasaha na hukumar NFF Ahmed Fresh Yusuf, ya ce kowanne dan wasan Eaglets zai sami Kyautar dalar Amurka dubu $ 5,600 kwatancin Naira miliyan N2m) ko fiye da haka idan har suka samu nasara a wasan ta ranar asabar.
A ranar Laraba da ta gabata ne daddare 'yan wasan Eaglets suka doke masu masaukin baki kasar Niger da ci 2-1 a wasan kusa da na karshe kuma an ba kowanne dan wasa kyautar dala dubu $ 2,800.
Ku Duba Wannan Ma Shugaban Laberiya Geoge Weah Ya Taka Ledar Minti 79Da yake jawabi akan wasan mataimakin mai horas da kungiyar Nduka Ugbade wanda kuma tsohon danwasan Najeriya ne a shekarun baya ya ce tawagar ta 'yan kasa da shekara 17 za ta yi kokari don tabbatar da cewa sun doke Ghana, a wasan karshen.
"Abinda ke gabanmu yanzu shine mu fara gyara wasu abubuwan da muka gani ba daidai ba a cikin wasannin da mukayi baya. Ya kara da cewar idan har 'yan wasan za su saurari bayani da kuma aiwatar da umarnin da aka ba su, to zamu doke Ghana a wasan karshe.
A ranar Asabar ne za'a buga wasan karshen da karfe 7 na yamma, haka kuma a ranar ne za'a fafata a wasan matsayi na uku a tsakanin masu masaukin baki Nijar da Cote d'Ivoire da misalin karfe 4pm, duk a filin wasa na Seyni Kountche a Niamey jamhuriyar Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5