Hukumar NFF Ta Karrama 'Yan Kwallon Najeriya

An zabi dan wasan gaba na Super Eagles dake tarayyan Najeriya Ahmed Musa, a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na Najeriya na shekarar 2018.

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Najeriya ke shiryawa a duk shekara, don zakulo 'yan wasan da sukayi kokari, a bana an yi taronne a birnin Ikko, a dakin taro na Eko Hotels & Suites ranar Litinin 1 ga watan Afirilu 2019.

Ahmed Musa wanda tsohon dan wasan Leicester da CSKA Moscow ne, a yanzu yana taka ledarsa a kungiyar kwallon kafa ta Al-Nasrr dake kasar Saudiya, ya haura kan takwarorinsa irin su Odion Ighalo, na Shanghai Shenhua, da kuma dan wasan gaba na Arsenal, Alex Iwobi.

Musa ya samu wannan nasaranne bisa irin kokarin da yayi musamman a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ya gudana a Rasha cikin shekarar 2018.

Haka zalika shine dan wasan da aka zaba wanda ya jefa kwallo mafi kyau a 2018, a wasan da yaci kasar Iceland na cin kofin duniya.

Hukumar ta NFF ta zabi gwarzayen shekara a fannin daban-daban, ciki har da bangaren Mata inda aka zabi Onome Ebi, a matsayin gwarzuwar 2018, bangaren Mata.

Sauran wanda aka zaban sune kamar haka. Akwai Super Falcons wato Mata a matsayin kungiyar kwallon kafa mafi kyau a 2018.

An zabe Samuel Chukwueze, a matsayin matashin dan wasa a 2018, sai bangaren mata kuma Anam Imo. A bangaren masu horas da 'yan wasa kuwa akwai Gbenga Ogunbote a sashin kungiyar Maza, da kuma Thomas Dennerby, bangaren Mata.

Har ila yau magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars su suka lashe kyautar ta bana a matsayin gwarzaye, sai Akwa United kyautar Fair Play.