Hukumar NDLEA Ta Kama Muggan Kwayoyi A Jihar Filato

NDLEA LOGO

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a jahar Pilato tace ta kame muggan kwayoyi masu nauyin fiye da kilogram dubu uku da dari biyu da goma sha bakwai da suka hada da tabar wiwi, hodar ibilis da wadansu kwayoyi masu bugarwa kamar maganin tari na kodin.

Kwamadan hukumar a jahar Pilato Ngozi Madubuike tace a shekarar da ta gabata hukumar ta cafke mutane dari uku da tamanin da shida da suka hada da mata goma sha bakwai.

A cewar Madam Ngozi, babban kotun tarayya dake Jos ta yanke wa mutane tasain da shida hukuncin dauri, yayinda hukumar ta taimaka wa wasu masu shan kwaya arbain da biyu da horo kan yadda zasu daina shan kwayar su kuma taimakawa rayuwarsu da sauran alumma.

Ta ce ‘yan mata da dama sun shiga karuwanci ta dalilin shan kwayoyi dake gusar musu da hankali.

Kan haka Kwamandar tace shan miyagun kwayoyi na da nasaba da fashi da makamai, tashe tashen hankali da matasa ke aiwatarwa, fyade, gushewar hankali a wasu lokuta har ya kai ga mutuwa.

Madam Ngozi ta bukaci masu ruwa da tsaki wajen yaki da manyan masu fataucin kwayoyin da masu nomawa da ma masu saidawa a tsakainin alumma su taimaka.

Kwamishanan mata da walwalar jama'a a jahar Filato, Rufina Gurumyen ta bukaci alumma, shugabannin addinai, makarantu da iyaye da su kula da tarbiyyar ‘ya'yansu.

Tace matsalar shan kwayoyi, kwankwadar barasa, tashin hankali da tabarbarewar tarbiyya, abubuwane da suka addabi jama'a da gwamnati dake bukatar hadin kai wajen dakile su.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar NDLEA Ta Kama Muggan Kwayoyi A Jihar Filato - 1' 50"