Ba kamar yadda ya faru ba a 2023, wanda sakamakon rikicin da a ke yi a Sudan tsakanin shugaban gwamnatin kasar Janar Abdulrahman Burhan da shugaban sojojin sa kai Janar Hamdan Hemedti Dagolo ya sa aka yi zagaye, a 2024 za’a bi ta sararin samaniyar Sudan.
A shekarar da ta gabata abun ya kai ga sai da aka yi amfani da wasu daga cikin kudin guzurin maniyata, saboda zagayen da a ka yi ya jawo karin kudin kujerar.
Shugaban Hukumar alhazai ta NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ya bayyana cewa badi ba za’a fuskanci wannan kalubalen ba.
Duk da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki a Najeriya kuma ana shirin rufe karbar kudin a wannan watan, shugaban hukumar NAHCON yace ana samun nasara wajen karbar kudin kujerar da suka kai Naira miliyan 4.5.
Shugabar kamfanin Dija Travel, daya daga cikin kamfanonin jirgin yawo da zasu yi aikin hajjin 2024, Hajiya Amina Ibrahim Yusuf, ta ce zasu hada karfi da karfe da sauran kamfanoni don gudanar da aikin.
Hajiya Amina Ibrahim ta kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta duba lamarin farashin dala domin maniyata su samu sauki wajen biyan kudin kujerar.
Hukumar NAHCON dai ta sha alwashin inganta ayyukanta domin jin dadin alhazai.
Saurari rahoton Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5