Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Ayyana Dokar Ta Baci Game Da Cutar ZIKA

Pregnant women wait to be attended at the Women National Hospital in San Salvador, El Salvador, Jan. 29, 2016.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO a turance tace ta ayyana dokar ta baci game da cutar nan ta zika dake yaduwa kamar wutar daji.

Ita dai wannan cutar an dangata ne da haihuwa a kudancin Amurka, hukumar tace wannan cutar tana nema ta zama alakakai ga sauran sassan duniya.

Jiya ne dai hukumar ta dauki wannan matakin, tace duk da yake ba samu wata kwakkwarar hujja ba cewa sauro ne ke haddasa mummunar illa ba ga kwakwalwan jarirai musammam a Brazil bayan da cutar da barke a shekarar 2013-14.

Yanzu haka dai rahotanni sun tabbatar cewa ciwon kwakwalwa wanda ke karuwa cikin jarirai wadanda suka kamu da cutar sai kara bazuwa yake yi a sassan da wannan cutar ta barke.