Hukumar Kwastan Tayi Wawan Kamu a Legas

Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Reshen hukumar kwastan dake kula da yankin yammacin ruwan Najeriya ya kama buhunan tabar wiwi sittin da biyu da aka kyasta kudinsu ya kai Naira miliyan dubu dari hudu da dubu dari biyar.

An yi yunkurin shigo da tabar ne daga kasar Ghana ta hanyar tekun wajejen jihar Legas.

Babban kwamanda mai kula da yankin ruwan tekun Najeriya Umar Yusuf yace kamun ya biyo bayan sintiri ne da jami'an kwastan keyi a yankin ruwan Ojo da Alaba ba dare ba rana.

Kwamandan yana mai cewa sun kama tabar amma kodayake basu kama mutane ba suna nan suna anfani da wadanda suke samar masu labaran siri su cigaba da cigiya. Haka ma hukumar NDLEA ta baza jami'anta suna nan suna bincike.

Ana shigo da tabar daga kasar Ghana saboda masu shanta sun tabbatar tafi ta Najeriya karfi. Matasa su ne suka fi sayen tabar.

Wani matashi yace yana farin ciki tare da bada goyon bayansa ga hukumar kwastan da kamun da tayi musamman a Najeriya, kasar da take fama da matsaloli daban daban. Yace matasan Legas suna shaye shaye har wasu ma suna haukacewa. Idan aka cigaba da samun irin kamun za'a shawo kan matsalar.

Ita hukumar kwastan din tana aiki da sojojin kasa da na ruwa da ma NDLEA, hukumar dake yaki da safarar muggan kwayoyi.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastan Tayi Wawan Kamu a Legas - 3' 08"